Majalisun dokokin Najeriya zasu yi mahawara kan kundin zaben kasar

Nigeria
Image caption Farfesa Attahiru Jega

Kundin dokokin zaben Najeriya

A Najeria yau ne ake sa ran majalisun dokokin kasar zasu yi mahawarar amincewa da sauye -sauye ga kundin dokokin zaben kasar na 2006.

Wannan ya biyo bayan zaman da kwamitin hadin gwiwa kan sauya dokokin zaben kasar yayi inda ya amince da sauye sauyen.

Daftarin da za'a gabatarwa majalisun a yau dai ,ya kai shafuka dari uku kuma ya kunshi gyaran fuska ga dokokin da ake dasu ,dama sababbin dokoki.

Honarable Musa Sarkin Adar wanda memba ne, a kwamitin hadin gwiwar da yayi aiki kan sabon daftarin ya fada wa BBC cewa, idan an amince dashi a yau, to sunan daftarin zai sauya zuwa kundin dokokin zabe na 2010.