An nada sabon sarkin Bauchi

Image caption Najeriya

A nada sabon sarkin Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya ta sanar da Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu a matsayin sabon sarkin Bauchi.

Sabon sarkin ya gaji mahaifinsa ne, Alhaji Suleiman Adamu wanda Allah ya yi wa rasuwa makon da ya gabata.

Alhaji Rilwanu suleiman Adamu yanzu shi ne sarkin Bauchi na goma sha daya.

A shekarar 1970 aka haifi mai martaba Alhaji Rilwanu, kuma baya ga ilimin firamare da sakadanre sabon sarkin ya samu shaidar malanta wato NCE daga kwalejin fasaha ta Bauchi

Ya kuma samu digri a fasahar gine-gine a jami'ar Abubakar Tafabalewa dake jihar Bauchi.