Majalisun dokokin Najeriya sun aminnce da yiwa dokokin zabe garanbawul

Nigeria
Image caption Farfesa Attahiru Jega

Majalisun dokokin Najeriya sun amince da wasu gyare-gyare da suka yiwa dokar zaben kasar.

Yawancin gyare-gyaren dai sun shafi batutuwa ne da suka hada da yadda hukumomin zabe na kasa da jihohi za su gudanar da ayyukansu.

Hakan nan kuma akwai batun sake ka'idojin yin rajistar jam'iyyu.

Wannan ya biyo bayan zaman da kwamitin hadin gwiwa kan sauya dokokin zaben kasar yayi inda ya amince da sauye sauyen.

Daftarin da aka gabatarwa majalisun a yau dai ,ya kai shafuka dari uku kuma ya kunshi gyaran fuska ga dokokin da ake dasu ,da ma sababbin dokoki.