Amurka ta roki Wikileaks ya daina buga takardun sirri

Bayanan sirrin na barazana ga tsaron Amurka
Image caption Shugaban Amurka,Barack Obama

Hukumomi a kasar Amurka sun roki shafin intanet na Wikileaks,wanda ya wallafa takardun sirri akan yakin Afghanistan, ya dakatar da yin hakan.

Kakakin fadar White House,Robert Gibbs ya jaddada korafin da manyan jami'an sojan Amurka suka yi cewa fitar da takardun sirrin na barazana ga tsaon kasar.

Ya kara da cewa wallafa takardun zai saka sojan Amurkan da kuma masu basu bayanai a Afghanistan cikin hadari.

Mista Gibbs ya ce Amurka za ta dorawa shafin na Wikileaks alhakin duk barazanar tsaro da wallafa takardun sirrin ta jawo ga mata.

Sai dai wanda ya kirkiro shafin,Mista Julian Assange ya yi watsi da zargin,inda ya ce shafin ya yi hakan ne don tabbatar da adalci

Zuwa yanzu dai shafin na wikileaks ya wallafa kimanin takardu dubu saba'in da biyar,wadanda ke nuna abubuwan dake faruwa a fagen daga,da kuma yadda ake samun bayanan sirri.