Kwamati ya bada shawarwari kan hana aukuwar gobara a Australia

Gobara ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Australia
Image caption Gobara ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Australia

Kwamatin da hukumomin kasar Australia suka kafa don yin binkice akan masabbin tashin wata mummunar gobara a kasar ya bada shawarwari guda 67 kan yadda za a kaucewa irin abinda ya afkun a nan gaba.

Shawarwarin na kunshe a cikin rahoton da kwamatin ya mikawa hukumomin kasar.

Kwamatin maisuna Royal commission ya baiwa hukumomi shawara da su gina gidajen ko-ta-kwana a sassan da gobara ka iya afkawa, sannan ta fitar da wani tsari na kwashe mutane daga wurin idan hakan ta faru.

A nata bangaren, gwamnati ta yi alkawarin aiwatar da shawarwarin da kwamatin ya bayar

Mutane 173 ne suka mutu, sa'annan daruruwan gidaje suka kone a jihar Victoria dake yammacin kasar a watan Fabrairun shekarar 2009.