Shugabannin Syria da Saudi a Lebanon

Sarki Abdullah da Shugaba Assad
Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya da Shugaba Assad na Syria.

Sarki Abdullah na Saudiyya da Shugaba Bashar Al-Assad na Syria sun kai wata ziyara ta hadin gwiwa zuwa Lebanon, a wani yunkuri na sasanta zaman dardar da ke ta karuwa tsakanin mabiya akidoji daban-daban na addini.

Syria, wadda ke goyon bayan kungiyar Hizbullah ta 'yan Shi'a, da kuma Saudiyya da ke da tasiri mai yawa a kan mabiya Sunnah na kasar, sun kuduri aniyar yin aiki tare don kauce ma aukuwar sabon rikici a kasar.

Wani mutum a Beirut, babban birnin kasar, yana ganin ziyarar wata alama ce ta kyautatuwar al'amurra tsakanin Syria da Lebanon.