Sarkin Saudiya da shugaban Syria na ziyayar Lebanon

Image caption Sarki Abdullah da shugaban Syria

A yau ne sarki Abdallah na Saudiya da shugaba Bashar al-Asad na Syria ke isa kasar Lebanon a wata ziyarar hadin gwiwa mai cike da tarihi.

Wannnan ce ziyarar shugaba al-Asad ta farko zuwa Lebanon, tun bayan kisan gillar da aka yiwa tsohon firaminista Rafik al-Hariri shekaru biyar da suka wuce-wanda aka zargi Syria da alhakin yi har ta yi sanadiyyar janye dakarunta daga Lebanon.

Ziyarar ta zo ne daidai lokacinda rahotanni ke cewa wata hukumar bincike ta kasa da kasa na shirin tuhumar wasu yan kungiyar Hizbullah ta Lebanon da laifin aikata kisan gillar, abinda zai iya haddasa sabon rikici tsakanin yan shi'a da Sunni a kasar.

Wakilin BBC ya ce Saudi Arabiya na daukar kanta a matsayin mai kare mabiya Sunna, yayinda Syria mai dangantaka da Iran ke da kusanci da Hizbullah.

Don haka wannan ziyarar hadakar ke da muhimmanci sosai, kuma yan Lebanon da dama na fatan za ta iya kashe wutar rikicin da ka iya kunno kai tsakanin bangarorin biyu.