Hukumar Interpol na nazarin auren Yerima

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Najeriya ta ce, hukumar 'yan sanda ta duniya, watau INTERPOL, ta yarda ta gudanar da bincike akan zargin da ake yi wa Sanata Ahmad Sani Yarima, na auren wata yarinya, 'yar kasar Masar, wadda aka ce ba ta isa aure ba.

Auren dai ya janyo kace-nace a Najeriya, har ta kai majalisar dattawa ta kafa wani kwamiti domin ya gudanar da bincike a kan batun.

To amma a cewar Senata Ahmad Sani Yarima, bai aikata wani laifi ba, tun da dai bai yi abinda ya sabawa addininsa ba.

Ya kuma ce shekarun yarinyar da ya aura sun haura sha ukun da ake magana.