Baraka na barazana ga jam'iyyar PDP a Kaduna

Taswirar Najeriya
Image caption Da sauran rina a kaba

A Najeriya jam'iyyar PDP mai mulkin jahar Kaduna ta shiga wani sabon rudu tunda uwar jamiyyar ta yi shelar cewa gwamnan jahar na yanzu shi zai kasance dan takarar jamiyyar a zaben shekarar 2011.

Jam’iyyar ta yanke wannan hukunci ne a wani taron masu ruwa da tsaki na jamiyyar wanda ya sami halartar wasu manyan yayanta na jahar.

To amma wannan taro ya bar baya da kura, inda wasu ke cewa ba a yi musu adalci ba, domin ba ta waccan hanya ake fitar da yan takara ba.

Abin ya kai har wasu ‘yan jam’iyyar suna barazanar kaurace mata.