Mataimakin gwamnan Abia ya yi murabus

Taswirar Najeriya
Image caption Ana yawan samun rashin jituwa tsakanin gwamna da mataimakinsa a Najeriya

A Najeriya, mataimakin gwamnan jihar Abiya, Mista Chris Akomas ya sauka daga mukaminsa.

Ya shaidawa manema labarai ranar asabar cewa ya yi murabus ne domin ya tsira da mutuncinsa.

Sai dai masana harkokin siyasar jihar na ganin cewa ayije mukamin nasa ba zai rasa nasaba da takun sakar da ya dade yana yi da gwamnan jihar,Mista Theodore Orji bisa bambancin ra'ayin siyasa.

Tun da farko dai majalisar dokokin jihar ta ce ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan, sai dai bangaren gwamnan jihar Abiyan ya ce bai san da wannan batu ba.