Gwamnati da likitoci na cece-kuce a Jigawa

Taswirar Najeriya
Bayanan hoto,

Likitoci,da hukumar asibitin Birnin Kudu na sa'insa kan albashi

A Najeriya,kananan likitocin dake aiki a asibitin tarayya dake Birnin Kudu a jihar Jigawa sun koka kan rashin biyansu albashi.

Likitocin sun ce hukumar asibitin ta hana su albashin watan Yuni,dana Yuli, sakamakon shigarsu yajin aikin gama-gari da kungiyar likitoci ta gudanar a watan da ya gabata.

Sai dai hukumar asibitin ta ce ta hana likitocin albashin ne saboda ba sa cikin wadanda ya kamata su tsunduma cikin yajin aikin tunda farko.

Sai dai 'yan jihar sun yi kira ga bangarorin dake rikicin su gaggauta sulhunta tsakaninsu kafin batun ya shafi yanayin tafiyar da asibitin.