Cuba ba zata sauya tsarin tattalin arzikinta ba, in ji Castro

Shugaban kasar Cuba,Mista Raul Castro
Image caption Castro ya ce Cuba bata da niyyar gudanar da sauyi a tsarin tattalin arzikinta

Shugaban kasar Cuba, Raul Castro,ya ce gwamnatinsa bata da niyyar bullo da sauye sauye a fannin tattalin arzikinta.

Sai dai ya ce gwamnatin na shirye-shirye na barin ma'aikata su zama masu dogaro da kansu ta hanyar kafa kananan sana'oi.

A jawabin da ya yiwa majalisar dokokin kasar,wanda aka yada ta gidan talabijin,Janar Castro ya ce gwamnatin za ta dauki matakan gaggawa wajen zaftare tsarin biyan albashin kasar.

Ya ce tsarin tattalin arzikin kasar ya inganta ne saboda goyon bayan da ya samu daga yawancin jama'ar kasar.