Direbobi a kasar Girka sun ba da kai

Turar kasar Girka
Image caption Za a koma tattaunawa

Direbobin manyan motoci a kasar Girka sun kawo karshen matsanancin yajin aikin da suka kwashe mako guda suna gudanarwa, kuma za su koma tattaunawa da gwamnati.

Matakin da kungiyar direbobin ta dauka,ya zo ne bayan da gwamnati ta kaddamar da wata doka wadda za ta ba ta ikon yin amfani da manyan motocin da ma kuma tilasta ma direbobin komawa bakin aiki.

Giorgos Tzortzatos, wakili ne na kungiyar direbobin.

Ya kuma ce “Bisa la'akari da matsalar da aka shiga, sakamakon rashin kai kayan abincin kasuwa da kuma rarraba man fetur, mun janye yajin aiki, da karamin rinjaye.”

An fara yajin aikin ne ranar Litinin, game da shirin bude harkar sufurin ga kowa, domin kara samun gogayya, kamar yadda asusun lamuni na duniya ya nema.