An yi sauyi a Majalisar dokokin Adamawa

Rahotanni daga jihar Adamawa ta Nijeria sun ce kakakin majalisar Mr James Barka da kuma mataimakinsa Aliyu Isa Amadu sun rasa mukamansu.

Hakan ya faru ne bayan da 'yan majalisar suka yi kokarin tsige su, sai kakakin majalisar ya yi murabus nan take, yayinda aka tsige mataimakinsa.

An maye gurbin kakakin da Mr Gibson Nataniel da kuma sabon mataimaki Alpha Belel.

Duk da yake cewa, dukkansu 'yan jam'iyyar PDP ne, amma ana yi wa sabbin shugabannin majalisar kallon wadanda ke adawa da Gwamna Murala Nyako na jihar, yayinda wadanda aka sauke kuma ake cewar suna dasawa da shi.