Kungiyoyi na shakku kan zabe a Nijeriya

A Najeriya kungiyoyin farar-hula sun fara nuna damuwarsu dangane da abin da suka bayyana da halin ko-in-kula da bangaren zartarwa ke nunawa game da bukatar da hukumar zaben kasar ta gabatar ta neman naira biliyan saba'in da hudu domin ta iya shiryar babban zaben kasar na badi.

Kungiyoyin dai sun ce hankalinsu ya tashi sosai ganin cewa lokaci sai kurewa yake yi, amma gwamnati ba ta ce uffan ba dangane da wannan bukata.

Ita dai hukumar zaben ta yi kashedin cewa idan kudaden ba su samu a cikin makonni biyu ba, to zai yi wuya ta iya gudanar da zabe da sabuwar rajistar masu kada kuri`a a watan Janairu mai zuwa.