Zaurawan Iraqi sun kai miliyan guda

Zaurawa a Iraqi
Image caption Daya dagha cikin zaurawan Iraqi tana tare da danta, wanda ke fama da matsala

Yakin da aka dade ana gwabzawa dama wanda ake fafatwa yanzu haka a kasar Iraqi, ya sanya adadin zaurawa a kasar ya haura miliyan guda.

Wasu alkaluma da hukumomi suka fitar a kasar sun nuna cewa adadin zaurawan ya kai sama da miliyan guda sakamakon yake-yaken da kasar ta yi fama da su.

Wasu daga cikin zaurawan da sashin BBC na Larabci ya tattauna da su, sun bayyana yadda matsalar ke ci musu tuwo a kwarya, da kuma fatan da suke da shi a nan gaba.

Elham Mahdi:

Wata bazawara ce a birnin Baghdad da ke da shekaru 42, kuma ta shaidawa BBC cewa:

Na zamo uwar marayu hudu ne lokacin da mijina ya rasu a wani harin bom da aka kai a motar bus lokacin da yake tafiya aiki.

Tace ya bar gida ne da misalin karfe takwas na safe, domin zuwa kasuwar Shorja inda yake aiki, amma bayan sa'a daya da rabi shi kenan sai labari.

Image caption Elham bazawara ce da mijinta ya rasu ya barta da 'ya'ya

Mun karbi diyya daga gwamnati, amma ba za ta maye gurbin mutumin da 'ya'yansa ke matukar kaunarsa ba.

Muna karbar kudi daga gwamnati duk bayan watanni shida, amma ba sa iya biyan bukatunmu.

Duk da cewa ina samun taimako daga kungiyoyin faras hula abisa karatu da kuma tufafin yara na, har wayau ina bukatar karin taimako domin lura da wadannan yaran.

Razan Othman Muhammad:

Ma'aikaciya ce 'yar shekaru 29 a birin Baghdad, kuma ta ce:

Bayan shafe shekaru goma muna soyayya da miji na, amma cikin minti daya na rasa shi. A shekara ta 2008 ne wani harin bom ya ritsa da mu a wata kasuwa.

Na fita a hayyaci na, kuma nan take mijina ya rasu akan hanyar tafiya da shi asibiti, yaranmu ma ya samu rauni, kuma har yanzu ba ya iya tafiya.

An yi mini tiyata har sau biyar, ban san mijina ya rasu ba sai bayan wata uku, saboda likitoci sun nemi da kada a gayamini.

Image caption Mazaje da dama ne suka rasu sakamakon yaki a Iraqi

Tun daga lokacin na koma gida ina zama tare da iyayena, amma ina cikin yanayi mai kyau idan aka kwatanta da sauran zaurawan dake kasar nan.

Ya kamata gwamnati ta dauki mataki kan wannan kaso na jama'a wadanda yanzu adadinsu ya kai miliyan guda.

Nahla Al Nadawi, malama ce a jami'ar birnin Baghdad mai shekaru 44, kuma ta ce ranar binne mijinta ita ce mafi tsauri a rayuwarta.

Ban samu damar yin wani abu na azo a gani ba, saboda babu mai kula da yaran mu idan bani da miji na ba.

Mijina dan gudun hijira ne a Jamus, amma bayan samun sauyin shugabanci ya dawo gida a shekara ta 2003. Kuma a shekara ta 2007 ne aka kashe shi awani harin kunar bakin wake da aka kai a gadar Al Jadiriyah da birnin Baghdad.

Ina bukatar dauki domin samun damar lura da dana a matsayinsa na mai bukatar kulawa ta musamman, saboda matsalar da yake da ita.

Adawiyya Mukhtar Hussein:

Bazawara ce mai shekaru 40 da haihuwa, ta shaidawa BBC cewa:

Na rasa mijina lokacin da nake da juna biyu, 'yata wacce ke da shekaru shida ta zamo marainiya tun kafin a haifeta.

An kashe mijina a shekara ta 2004 a wani rikici na dangi, kuma ya barni da yara biyu da nake lura da su ni kadai.

Na yi kokarin samun hakkin mijina amma babu mai tallafamini, gwamnati ba ta da karfi a lokacin, don haka ba kowa ne ke son ya shiga cikin irin wannan rikicin ba.

Hayar samun kudi kawai ita ce ta samun taimako daga makwafta da kuma share-sharen da nake yi a wuraren biki ko fati.

Na nemi taimakon kudi daga gwamnati amma bayan shekarau shida da rasuwar mijina, har yanzu ban ji komai ba.

Kusan baki dayan abinda nake samu na tafiya ne wajen biyan hayar gidan da nake ciki, wanda daki daya ne kacal.