Dan China zai sayi Liverpool

Gerrard
Image caption Kaptin din Liverpool Steven Gerarrd

Nanda 'yan kwanaki akwai alamun wani attajirin dan kasuwa daga China zai sayi kungiyar Liverpool ta Ingila.

Kenny Huang wanda shine shugaban kampanin bunkasa kasuwanci na Hong Kong na son ya mallaka daukacin kungiyar Liverpool wacce aka sanya a kasuwa tun watan Aprilun daya wuce.

Wata majiya ta shaidawa BBC cewar "za a cimma yarjejeniya kafin 31 ga watan Agusta".

Huang dai ya shafe makwanni ya tattaunawa da wakilan Bankin Royal na Scotland don karbe madafan iko a Liverpool.

Bankin dai shine wanda ya baiwa Amurkawan nan wadanda suka mallaki Liverpool wato Tom Hicks da George Gillett bashin kusan pan miliyan 237.