Hadin kan 'yan kasar Nijar

'yan Nijar na da kishin kasa
Image caption 'yan Nijar na da kishin kasa

Tun bayan samun yancin kai daga turawan milkin malaka kasar, Nijar ke iya nata kokari na ganin kasar bata fada cikin matsalolin da suka shafi rikici kamar su yakin kare dangi na kabilanci, ko na addini kamar yadda da dama ake samu daga cikin wasu kasashe Afrika.

Sai dai gwamnatin kasar tayi fama da tawayen Buzaye dana tubawa , na wani lokaci .

Kasancewar al'umar kasar ta Nijar ba al'umma bace mai son tashin hankali tare da kokarin kasahen ketare da suka yita kai komo wajen ganin kasar ta kai karshen wannan matsalan da ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama wanda su ka hada da Sojoji da fararen hula dasu yan tawayen .

Hakan dai bayi dadi ba kasar mai kabilu daban daban , da kuma kusan suka sade sanadiyar aure tsakanin kabilun hakan yasa kusan kowace kabila ta kasar Nijar nada abokiyar wasa .

Ba'idin arataya tsakanin kabilu a shekara ta 1979 gwamnatin mulkin sojin lokacin karkashin shugabancin marigayi tsohon shugaban kasa Seini Kunce ta kirkiro da wasu wasani matattara matassa da ake kira festival de la jeunesse.

Da kuma kokowar gargajiya wadannan wasani na ba matassan jamhuriyrar Nijar dammar gamuwa kowace shekara cikin wata jaha inda za'a kwashe kwananki ana wasanni daban daban .

Ta haka ma a kasar ta Nijar Musulmi da kristoci nada hadin kai inda suke kokari wajen wayar wa vmutanensu da kai kan zaman tare kamar yanda pasto Haruna Labo ya shaida mani.

Al'umar jamhuriyar Nijar da wakiliyar BBC ta zanta da su, sun nuna jin dadin na kasancewar su yan kasar duk da dumbin matsalolin da suka dabaibaye ta , to amma tunda da kwanciyar hankali suka ce shine babban arzikin wannan kasa .