Ta leko ta koma ga masu neman aikin 'yan sanda a Kano

Wasu 'yan sandan Nijeria
Image caption Wasu 'yan sandan Nijeria

A Nigeria, aikin tantance mutanen da za'a dauke su a aikin 'yan sanda ya ci karo da mastala a jihar Kano dake arewacin kasar.

Masu neman aikin ne dai da dama suka halarci hedkwatar rundunar 'yan sandan jihar tun da safiyar yau domin ci gaba da aikin tantance su, amma sai aka shaida musu cewa ba za'a ci gaba da aikin ba a yanzu, don haka su koma gidajensu sai an neme su.

Masu neman aikin dai sun fito ne daga sassan jihar daban daban.

Rundunar 'yan sandan ta Nigeria dai ta kuduri daukar mutane dubu arba'ain cikin rundunar, da nufin kara samar da tsaro a kasar, tare kuma da cike gurbin wadanda suke barin aiki.