Ana ci gaba da agazawa jama'a a Pakistan

Ambaliyar ruwa  a Pakistan
Image caption Sama da mutane dubu daya ne suka rasa rayukansu a wannan bala'in

Ma'aikatan agaji a Pakistan suna ta faman kai kawo domin isa wurin wadanda suka tsira daga ambaliyar ruwa mafi muni da aka gani a cikin shekaru.

An tabbatar da rasuwar akalla mutane dubu da dari daya sun rasa rayukansu.

Wani kakakin kungiyar agaji ta Save the Children ya bayyanawa BBC cewa, barnar da ambaliyar ruwan tayi na da yawa musamman a kwarin Swat, wanda ake ganin har ya haura barnar da girgizar kasa tayi wa yankin a shekara ta 2005.

Dakarun sojin Pakistan sun ce suna bakin kokarin tallafawa duk wadanda ke cikin matsi sai dai har yanzu akwai dubunnai da ke jiran gawon shanu.

Babban kalubalen da masu aikin agajin ke fuskanta shi ne na rashin kyawun hanya.

Image caption Taswirar yankunan da ambaliyar ruwan ta Pakistan ta mamaye

Ministan yada labara na Pakistan, Qamar Zaman Kaira, ya ce abin yafi tsanani a yankin Arewa maso yammacin kasar inda fiye da mutane miliyan daya da rabi ke bukatar agaji.

Yace idan yanayi babu kyau, jirage masu saukar ungulu ba su iya tashi, ga shi kuma hanyoyi da tituna da gadoji, duk ruwa ya shafesu.

Sai dai wadanda suka rasa duk abinda suka mallaka wasu ma har da danginsu, yanzu kuma suna fuskantar barazanar yaduwar cututtuka.

Abinci ya yi karanci kuma ambaliyar ta gurbata ruwan sha.

Marjan Khan, manomi ne a kauyen Charsada da ke lardin Khyber Pakhtoonkhwa.

Image caption Wani jirgin sama na tallafawa wadanda abin ya ritsa da su

Ya kuma ce: "Muna wanke ragowar alkamarmu ne wacce kusan ta gama lalacewa. Ba mu da komai kawai mun dogarane da rahamar ubangiji amma babu abinda ya rage mana banda alkamar."

Amma wani manomin mai suna Habib Gul da ke zaune a wani sansanin ba da tallafi tare da iyalinsa ya ce su kam babu abinda suka rasa.

Yace muna samun shinkafa dafaffiya, da wutar lantarki da ruwan sha. Bamu da wata matsala anan.

Sai dai suma kamar sauran dubunnan daruruwan mutanen da ke Arewa maso yammacin Pakistan, na ci gaba da taraddadin yadda za su sake gina rayuwarsu.