Ganga miliyan biyar ne ya kwarara a tekun Mexico

Kamfanin mai na BP
Image caption Injiniyoyin kamfanin mai na BP sun dade suna aiki domin shawo kan matsalar

Masana kimiyya na gwamnatin Amurka sun amannar cewa, yanzu kimanin ganga miliyan biyar na danyen mai ne ya kwarara daga rijiyar man kanfanin BP a tekun Mexico kafin a shawo kan al'amarin makonni biyu da suka gabata.

Hakan dai na nufin cewa, hadarin na iya kasancewa mafi muni na kwararar danyen mai a tarihi.

A yankin mashigin tekun Mexicon dai kamfanin mai na BP na daukar matakan karshe na toshe rijiyar ta hanyar amfani da laka da siminti.

Bayan da aka like rijiyar da ke tsiyaya, kuma ake saran tosheta kwata-kwata nan bada jimawa ba, wannan ka iya zamowa alkaluma na karshe.

Nan gaba a yau ne ake saran kamfanin BP zai yi gwajin karshe kafin a dauki matakin toshe rijiyar da siminti.

Kamfanin na BP ya samu kansa a cikin tsaka mai wuya, abin da yasa hannayen jarinsa suka yi ta faduwa, kuma nan gaba kadan ne Aka tsara shugaban kamfanin zai a jiye mukaminsa.

Wannan dai shi ne bala'in muhalli mafi muni da ya taba faruwa a tarihin kasar Amurka. Tuni dai kasar ta dakatar aikin hakar mai a karkashin teku, sai dai matakin na fuskantar kalubale ta fuskar shari'a.