Hizba ta lalata katan-katan na giya a Kano

Kwayoyi

A Nijeria hukumar Hizbah ta jihar Kano ta lalata katan dari shida da arba'in na giya, wadda aka kiyasta kudinta za su kai Naira Miliyan goma.

Hukumar tace ta farfasa kwalaben giyar ne a kokarin da take na kauda amfani da kayan maye a jihar ta Kano, da ke aiwatar da tsarin sharia'ar musulunci.

Jihar ta Kano dai ta yi kaurin suna wajen amfani da kayan maye, inda wani rahoto da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nigeria ya nuna cewa jahar ce kan gaba, wajen ta'ammali da miyagun kwayoyi da kayan sa maye.

A wannan karon dai hukumar ta warewa mata wannan rana ce domin su jagoranci lalata giyar sabanin a baya da maza ne kawai ke gudanar da aikin.