Ana nuna shakku kan zaben Najeriya

Shugaban Hukumar zabe Attahiru Jega
Image caption Hukumar zaben na cikin tsaka mai wuya muddum bata samu kudade a kan lokaci ba

A Najeriya yayin da ya rage kwanaki takwas wa'adin da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta debawa gwamnatin Najeriya na ta samarwa hukumar sama da Naira biliyan 70 ke cika.

Wasu kungiyoyin fararen hula a kasar na ganin cewar zaben kasar ka iya fuskantar barazana ganin cewar har yanzu gwamnatin Najeriyar ba ta sakarwa hukumar wadannan kudaden da ta nema ba.

Hakan kuma na zuwa ne daidai lokacin da majalisun dokokin Najeriyar suka fara hutunsu na shekara, lamarin da wasu kungiyoyi masu zaman kansu ke ganin zai kara dagula lamarin.

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta dai ta ce rashin samun wadannan kudade a iya lokacin da ta bayar ka iya shafar shirye-shiryen zaben dake tafe.

Amma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya shaidawa wakilin BBC Ibrahim Mijinyawa cewa a shirye majalisar take domin amincewa da kasafin kudin idan har bangaren zartarwa ya turomusu da bukatar yin hakan.

Ya kara da cewa za su iya katse hutun da suke yi a duk lokacin da gwamnatin ta nemi su amince da kasafin kudi na musamman domin baiwa hukumar zaben kudaden da take bukata domin gudanar da ayyukanta.