Za a gina masallaci inda aka kai harin 11 ga Satumba

Inda za a gina masallaci a New York
Image caption Wasu ba su ji dadin ba da iznin ba

Mahukunta a birnin New York sun amince da ginin wata cibiyar addini musulunci da ke kunshe da masallachi a daura da tsohuwar cibiyar ciniki ta duniya.

Masu ginin sun ce suna bukatar kafa cibiya ne ta kimanin dala miliyan dari mai hawa goma sha uku domin musulmi masu sassaucin ra'ayi.

Wakiliyar BBC ta ce shirin kuma ya kunshi gina wata alamar tunawa da wadanda harin sha daya ga Satumba ya rutsa da su.

Sai dai wasu daga cikin dangin mamatan sun ce gina masallaci daura da wannan wuri tamkar keta haddi ne game da wadanda suka mutu da kuma halin ko-in-kula.