Ana bikin cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai a Nijer

sojojin Nijer
Image caption sojojin Nijer

Yau ake bikin cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai daga kasar Faransa a Jamhuriyar Niger.

Hukumomin kasar sun takaita shugulgulan bikin wannan rana, tare da yin bukin dashen itatuwa da kuma jawabai ga yan kasa akasin bukukuwan ire iren wadannan ranaku a shekarun baya.

Gwamnatin mulkin soja ta kasar ta ce ta yi hakan ne domin taya 'yan kasar da matsalar yunwa ta addaba juyayin halin da suka tsinci kansu a ciki, tare da neman taimaka musu.