Mutum milyan 3 ambaliya ta rutsa da su a Pakistan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane miliyan uku ne ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru tamanin ta shafa a Pakistan.

Ko da yake kakakin sojin kasar ya shaida wa BBC cewa yanzu dakaru dubu hamsin sun samu isa wuraren da ke bukatar agaji,

Wadanda bala'in ya rutsa da su da dama na bayyana hushinsu kan yadda mahukunta suka gaza kai musu tallafi.

Yusuf Khan na daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa.

Ya kuma ce, “Gidana ya rushe sakamakon karfin ruwan sama da kuma ambaliyar, amma dai na tsirar da iyalina.

“Sai dai babu abinda zan ce game da gwamnatin Pakistan saboda babu wani abinda suke mana a wannan mawuyacin lokaci.”