An kama wani kusa a jam'iyyar MNSD-Nasara

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijer, Janar Salou Djibo
Image caption Janar Salou Djibo ya ce babu sani babu sabo a yakin da ya daura da cin hanci

A jamhuriyar Nijar hukumomin yan sanda sun kama tsohon Babban Darektan baitulmalin kasa, Malam Siddo Elhadj domin yi ma sa tambayoyi a kan wasu makuden kudade da suka salwanta yayin hajin bara.

Kwamitin da gwamnatin mulkin sojan ta kafa domin kwato dukiyar kasa ne ya tuhumi Malam Siddo Elhaj din cewa yana da hannu wajen karkata kudaden wadanda yawansu ya kai milliard ko biliyan biyu da rabi na CFA.

Sai dai jam'iyar MNSD Nasara ta Siddo Elhaj ta ce matakin, wani bi-ta-da-kullin-siyasa ne kawai.

Tun dai wani taron manema labarai ne da ya kira a farkon watan Yulin da ya gabata, kwamitin ya ambato sunan Siddo Elhaj daga cikin wadanda ake zargin suna da hannu a almundahanar.