Gwamnati ta nemi amincewar majalisa wajen baiwa INEC kudi

Goodluck Jonathan
Image caption Goodluck Jonathan

Gwamnatin Najeriya ta ce ta aikawa majalisar dokoki ta kasa wasikar neman sahalewarta domin baiwa hukumar zabe ta kasa - INEC Naira miliyan dubu saba`in da hudu domin shirye shiryen babban zaben da za a yi badi a kasar.

A cikin makon da ya wuce ne dai hukumar zaben ta gabatar da wannan bukatar.

Hukumar ta kuma yi kashedin cewar idan kudin ba samu ba cikin makwanni biyu, to kuwa da wuya ta iya gudanar da zabe a cikin watan Janairu mai zuwa da wata sabuwar rajistar masu zabe.

Hukumar ta ce, hakan kuwa zai iya tilasta mata yin amfani da tsohuwar rajistar dake cike da kura-kurai.

Tuni dai majalisar dattawa da ta wakilai ta ce zata kira zama na musamman domin tattaunawa akan bukatar gwamnatin.

Ana dai sa ran majalisun zasu amince da bukatar gwamnatin ganin yadda hukumar zaben ke neman wadannan kudade cikin gaggawa.

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Alhaji Bayero Nafada, ya ce majalisar wakilai zata tattauna domin ganin ko akwai bukatar ragewa ko karawa akan abun da gwamnatin ta gabatar.