Erastus Akingbola ya mika kansa ga EFCC

Takardar Kudin Naira
Image caption Takardar Kudin Naira

A Nijeria, yanzu haka tsohon shugaban bankin Intercontinental, Mr Erastus Akingbola wanda Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFFC ke nema ruwa a jallo, ya mika kansa ga hukumar.

Rahotanni dai sun nuna cewar Mr Erastus Akingbola ya koma Najeriyar ne a jiya domin amsa tuhumce tuhumcen da hukumomi ke yi masa.

Hukumar ta EFCC dai na zargin sa ne da halatta kudaden haram da kuma yin sama fadi da miliyoyin nairori.

A bara ne dai babban bankin Nigeria, CBN ya sallami shugabannin wasu bankunan kasar hudu ciki kuwa har da Mr. Akingbolan bisa zarge - zargen da suka hada da sakaci wajen bada bashi da kuma rashin aiki da ka'idodojin banki wajen sarrafa kudaden jama'a.