Saudiyya ta hana amfani da wayoyin Blackberry

Taswirar Saudi Arebiya

Hukumomin Saudi Arebiya sun bayar da umarnin a dakatar da amfani da wadansu hanyoyin sadarwa da na wayar salula kirar Blackberry daga ranar Juma'a mai zuwa.

Hukumomin Saudiyyar dai sun ce, wannan hani zai ci gaba da aiki har sai kamfanin kasar Canada da ke kera wayar ya cika wadansu ka'idojin yin rajista na kasar.

Tuni dai ita ma Hadaddiyar Daular Larabawa ta bayyana cewa tana shirin haramta amfani da wadansu hanyoyin sadarwa da ake samu a wayar kirar Blackberry domin hukumomin kasar ba sa iya sa ido a kan wadansu sakwanni da ake aikewa ta wayar.

Hukumomin dai sun bayyana cewa hakan na da alaka da batun tsaron kasa.