Shugaban Sudan na ziyara a Libya

Shugaba al- Bashir na Sudan
Image caption Shugaba al- Bashir na Sudan

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir ya fara wata ziyarar yini biyu a Libya a yau.

Ziyarar na zuwa ne bayan da Sudan ta rufe iyakarta da Libya a baya-bayan nan inda ta ce akwai bukatar yiwa dakarun tsaron iyakar garambawul saboda maida martani ga hare-haren yan tawaye.

Iyakar kasashen biyu dai ta ratsa ne ta yankin Darfur na kasar Sudan.

An dai samun karuwar zaman dar-dar ne tsakanin Sudan da Libya bayan da Libyan ta bada mafaka ga Khalil Ibrahim, jagoran daya daga cikin manyan kungiyoyin yan tawayen yankin Darfur, wato Justice and Equality Movement.