Mutanen Kenya sun amince da tsarin mulki

Masu kada kuri'a a Kenya
Image caption kashi biyu bisa uku na masu kada kuri'a sun amince da sabon kundin tsarin mulkin

Masu goyon bayan sabon kundin tsarin mulkin kasar Kenya sun yi nasara bayan da jama'a suka kada amince da kundin a kuri'ar rabagardamar da aka kada.

Bayan da aka bayyana sakamakon mafiya yawan kuri'un da aka kada, masu goyon bayan sabon tsarin mulkin sun samu rinjayen da ba za a iya cimmusu ba. Haka kuma masu adawa da shi sun amince da shan kayi.

Daya daga cikin masu goyon bayan tsarin Kiraitu Murungi, ya bayyana sakamakon da cewa wani muhimmin mataki ne da zai kai ga samun hadin kan kasar ta Kenya, da kuma shinfida wani tsarin dimokradiyya mai inganci a nahiyar Afrika.

Wannan zaben raba-gardamar dai wani zakaran gwajin dafi ne ga masu yekuwar samarwa kasar ta Kenya sabuwar alkiblar siyasa.

A zabukan da aka gudanar a shekarar 2007 dai bangarorin siyasa masu adawa da juna sun yi fito-na-fito, al'amarin da ya kai ga mutuwar fiye da mutane dubu daya.

Wadancan tashe-tashen hankulan ne kuma suka haifar da bukatar wannan sabon kundin tsarin mulkin, wanda ake ganin zai magance matsalolin da suka jawo rikicin tun da farko.

Inda aka samu bambanci kawai shi ne Lardin Rift Valley, inda kashi biyu bisa uku na masu kada kuri'a suka ki amincewa da sabon kundin tsarin mulkin.

Hakan kuma ya jefa ‘yar damuwa a zukatan wadanda ke fatan zaben raba-gardamar zai hada kan al’ummar kasar.