Naomi Campbell ta bayyana a shariar Charles Taylor

Naomi Campbell
Image caption Naomi Campbell ta ce ta karbi kunshin wasu duwatsu masu daraja, amma ba ta san ko wane ne ya ba ta su ba.

Fitacciyar mai amfani da surarta wajen tallata kayan ado, wato Naomi Campbell, ta shaidawa kotun sauraren karrakin laifukan yaki da ake zargin tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor cewa ta karbi kunshin wasu duwatsu masu daraja amma masu datti, a wani shagali da Nelson Mandela ya shirya a shekarar 1997.

To amma ta ce ba ta san ko wadanne irin duwatsu bane kuma ba ta san ko wane ne ya bata ba.

Ta ce a baya tana magana ne da Charles Tailor kan alamuranda suka shafi komi, saboda tana son sanin abubuwan dake faruwa a Liberia domin ba ta taba jin labarin kasar ba.