Majalisun Najeriya za su tattauna kudaden INEC

Taswirar Najeriya
Image caption 'Yan majalisun Najeriya sun ce za su yi duk abin da ya kamata don ganin hukumar zabe ta samu kudin da take bukata

Majalisun dokokin Najeriya sun ce a makon gobe ne za su yi wani zaman gaggawa domin yin muhawarar amincewa da kudin da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta INEC ke bukata domin sabunta rajistar masu zabe.

'Yan majalisar sun ce za su yi zaman ne ranar Talata mai zuwa domin su tabbatar da cewa hukumar ta INEC ta sami isassun kudaden da take bukata domin gudunar da wannan aiki.

Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majlisar Dattawan Najeriya, Sanata Ayogu Eze, ya bayyana cewa ‘yan majalisar za su tattauna ne a kan adadin kudin da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya aike musu, “saboda hukumar ba ta da hurumin neman kudi kai tsaye daga wurinmu”.

Ita ma Majalisar Wakilan kasar ta ce za ta dawo daga hutu don tattaunawa a kan wannan batu.

Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Usman Bayero Nafada, ya shaidawa BBC cewa: “Duk abin day a kamata a yi, Majalisa za ta zauna ta yi”.