An kama wata maata a Sakkwato bisa zargin fataucin mutane

'Yan sandan Nijeriya
Image caption 'Yan sandan Nijeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Sakkwaton Nijeriya a yau ta mikawa hukumar yaki da fataucin mutane wata mata 'yar kimanin shekaru arbain da kuma direban ta bisa zargin fataucin mutane.

Hukumar ta ce ta kama su ne yayinda suke kokarin tsallakawa da wasu yara shida zuwa cikin jamhuriyar Nijar a jiya.

Dukkanin yaran dai 'yan mata ne da shekarunsu suka kama daga 17 zuwa 19.

Matsalar safarar mutane dai ta jima tana ciwa hukumomin Nijeriya tuwo a kwarya.