Sabon shugaba a kasuwar hannayen jarin Najeriya

Dandalin kasuwar hanayen jarin Najeriya
Image caption Dandalin kasuwar hanayen jarin Najeriya

A Najeriya, hukumar dake sa ido kan kasuwar hada hadar hannayen jari ta kasar wato SEC, ta nada Mr. Emmanuel Ikazobah a matsayin shugaban wucin gadi na kasuwar hannayen jarin kasar.

Hakan dai ya biyo bayan sauke Darekta Janar ta kasuwar hannayen jarin ce, Farfesa Ndi Okereke daga mukaminta.

Har ila yau, hukumar ta dakatar da shugaban hukumar gudanarwa ta kasuwar hannayen jarin, Alhaji Aliko Dangote da sauran mambobin hukumar gudanarwar har sai an kammala sauraron karar dake gaban kotu dangane da zaben daya kaisu ga mukami.

Hukumar dai ta ce ta dauki wannan mataki ne da nufin karfafa guiwar masu zuba jari a kasuwar hada hadar hannayen jari ta kasar.

Nadin sabon shugaban na wucin gadi don tafiyar da harkokin kasuwar hannayen jari ta Najeriyar dai ya zo a dai dai lokacin da ake ci gaba da ce ce kuce dangane da yadda ake tafiyar da harkoki a kasuwar hannayen jarin.

Zargin sama da fadi

Wata sanarwa da ta fito daga hukumar dake sa ido kan kasuwar hada hadar hannayen jari ta kasar wato SEC, ta ce hukumar ta kwashe dogon lokaci tana nazari dangane da cece kucen da ake tayi akan zargin sama da fadi na wasu makuden kudade da kuma yadda ake tafiyar da harkokin kasuwar hada hadar hannayen jarin ta Najeriyar, wacce ita ce kasuwar hannu jari ta biyu mafi girma a nahiyar Afrika.

Image caption Tsohuwar Direkta janar din kasuwar da aka sauke, Dakta Ndi Okereke.

Hukumar ta kara da cewa ta dauki matakin sauke Darekta janar ta kasuwar hannayen jarin ce, Farfesa Ndi Okereke daga mukaminata da kuma dakatar da shugaban hukumar gudanarwa ta kasuwar, wato shahararren dan kasuwan nan, Alhaji Aliko Dangote, da wasu mambobin hukumar gudanarwar, domin maido da kimar kasuwar a idon masu zuba jari.

Sanarwar ta kara da cewa dakatar da shugaban hukumar da wasu mambobinta zai ci gaba har sai an kammala sauraron karar dake gaban kotu dangane da zaben daya kaisu ga darewa kan wannan mukami.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta bada umurni da a gudanar da cikakken bincike kan kudaden da ake zargin anyi sama da fadi da su a kasuwar hannayen jarin.

A kwanan dai rahotanni suka ambato shugaban hukumar gudanarwa da aka dakatar Alhaji Aliko Dangote, na zargin cewa ana kaucewa ka'ida wajen tafiyar da harkokin kasuwar hannayen jarin, lamarin daya ce ya sa kasuwar hannayen jarin ya tsiyace.

Ko a makon daya gabata sai da hukumar ta SEC ta yi barazanar gurfanar da wasu mutane hade da wasu kamfanoni 260 gaban wata kotu ta musamman, bisa zargin su da aikata ba daidai ba wajen sayar da hannayen jari a kasuwar, lamarin daya haifar da matsaloli ga bangaren wasu bankunan kasar.

Darajar hannayen jarin kasuwar dai sun fadi ne da kashi saba'in cikin dari a shekarar 2008 zuwa shekarar 2009, biyo bayan matsalar koma bayan tattalin arziki da kasashen duniya suka fuskanta.