Obasanjo ya zargi yan majalisar dokokin Nigeria

Olusegun Obasanjo
Image caption Olusegun Obasanjo

'Yan majalisun dokokin Najeriya sun mai da martani dangane da zargin da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya musu sun yi dumu dumu wajen cin hanci da rashawa a kasar.

A cewar shugaba Obasanjo 'yan majalisar sukan zake wajen binciken wasu `yan kasar game da cin hanci da rashawa alhali su ma sun yi dumu-dumu cikin al`amarin.

Tsohon shugaban kasar ya yi zargin cewa `yan majalisar na fakewa da sunan ayyukan raya mazabu wajen cusa wasu kudade a cikin kasafin kudi, inda suke zagawa su yi kashe-mu-raba da `yan kwangila.

Sai dai `yan majalisar a nasu bangaren sun musanta wannan zargi, saboda a cewarsu ba su da kusanci da yadda ake aiwatar da ayyukan raya mazabun.