Madam Patience Jonathan ta kaddamar da shirin zaburadda mata

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Uwargidan shugaban Najeriya Madam Patience Goodluck Jonathan ta kaddamar da wani shiri na tada kaimin mata wajen neman mukaman siyasa da kuma tashi tsaye domin a dama dasu a harkokin da suka shafi siyasa da sauran alamurra.

Taron da aka gudanar a Kaduna, ya sami halartar mata da dama daga ciki da wajen jihar, wadanda suka hada da matan wasu gwamnonin arewacin kasar, manyan 'yan siyasa mata, da sauran mata daga shiyyar arewa maso yamma na kasar.

Wannan shiri dai a ta bakin uwargidan shugaban kasar, zai fito da tsare tsaren da zasu taimakawa mata samun mukamai a kasar.

To amma yayin da ake kaddamar da wannan shiri,wasu na ganin a baya wasu matan shugabannin kasar sun sha bullo da shirye shirye to amma basuyi wani tasirin azo a gani ba.