Ra'ayi Riga: Shekaru hamsin da samun yancin kan Nijar, shin kwalliya ta biya kudin sabulu?

Bukin cika shekaru 50 da samun yancin kan Nijar
Image caption Bukin cika shekaru 50 da samun yancin kan Nijar

A ranar uku ga watan Agustan nan ne Nijar ta cika shekaru hamsin cif cif da samun 'yancin kai daga mulkin mallakar kasar Faransa.

Tun daga lokacin da Nijar din ta samu 'yancin kai, ta fuskanci kalubale da dama da suka hada da juyin mulkin soji har sau hudu, da matsalar tawaye da ta cin hanci da rashawa.

Nijar ta yi fama da matsalar karancin abinci a shekarun 1970 da 1984 da kuma shekara ta 2005, lokacin da mutanme kimanin miliya uku suka yi fama da matsalar tamowa.

Yanzu haka kuma, MDD ta ce kusan mutane sama da miliyan bakwai ne ke fuskantar matsalar karancin abinci a sakamakon fari .

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a baya-bayan nan, ya nuna cewa Nijar ce ke kan gaba a duniya a yawan masu fama da tallauci, kodayake a wasu lokutan gwamnatin kasar na nuna rashin gamsuwa da sakamakon irin wannan bincike.

Sai dai kuma wasu na ganin cewa kasar ta Nijer ta samu ci gaba a wasu fannonin da suka hada da kafa tsarin Demokradiyya mai jam'iyyu barkatai da kwato wa maata 'yancinsu da dai sauransu.

To domin duba wadannan kalubale mun kuma gayyato baki a cikin shirin, daga cikinsu akwai kakakin majalisar koli ta mulkin sojin Nijar, CSRD, Kanar Abdulkarim Goukoye.

Haka nan kuma akwai Ben Omar Muhammed, na tsofon kawancen jam'iyyun AFDR da ya yi mulki a Nijar din, da kuma Malam Bazoum Mohammed da shi kuma yake wakiltar kawancen jam'iyyun CFDR da yayi adawa da shirin Tazarce na tsohon shugaba Mamadou Tandja.

Haka nan kuma akwai Dr Souley Hassane na Jami'ar Poitiers a Faransa da kuma wasu daga cikinku, ku masu saurare.