Naomi Campbell ta bada shaida a kan Taylor

Naomi Campbell
Image caption Naomi Campbell

Fitacciyar mai amfani da surarta wajen tallata kayan ado, wato Naomi Campbell, ta shaidawa kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa-da-kasa wadda ke sauraron zargin da ake yiwa tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor, cewa ta karbi kunshin wasu duwatsu masu daraja amma masu datti, a wani shagali da Nelson Mandela ya shirya a shekarar 1997.

Sai dai kuma ta ce ba ta san ko wadanne irin duwatsu ba ne ba ta kuma san ko wanene ya bata su ba.

Wannan batu dai na ci gaba da jan hankalin jama'a a kasar Saliyo.

A baya dai kasar ta yi kaurin suna wajen kasancewarta cibiyar cinikin haramtattun ma'adanan lu'ulu'u da aka yi ta zubar da jini a kansu, kuma ya yi ta rura wutar tashin hankali a kasar.

Amma duka wannan ya kau a yanzu.

A wannan makon dai batun lu'ulu'un ne ya mamaye komai a kotun hukunta manyan laifuffukan ta kasa da kasa.

Brenda Hollis, wadda ta shigar da karar a wannan makon ce dai ta kirawo shaida ta daban--maimakon 'yan sari-ka-noken da kuma masu hakar ma'adanin, Naomi Campbell ta kira.

Ms Campbell ta ce a watan Satumban shekarar 1997 ta halarci wurin wata liyafa ta daya daga cikin kungiyoyin Nelson Mandela, wadda Mista Taylor ma da Mia Farrow da wadansu da suka yi fice suka halarta.

Bayan an kare liyafar ne kuma wani mutum ya kai mata ma'adanin lu'u lu'un wanda ake kyautata zaton ya fito daga wurin Mista Charles Taylor.

Ta ce wannan na nuni da cewa yana rike da irin ma'adanin lu'u lu'un da ake rikici a kansa. Wannan kuma ya saba da shaidar da ya bayar a gaban kotu cewa sam bai taba mallakarsa ba.

Yakin Saliyo dai ya yi matukar muni.

Shekarun Jabaty Mambu goma sha-shida a lokacin da 'yan sari ka noken RUF suka mamaye birnin Freetown.

"Gungun wadansu yara ne suka zagaye gidan mu.

"Sai suka ce kowa ya fito; suka kama ni, sannan suka kwantar dani a kasa, sai wani ya datse min hannu na na dama", inji Jabaty.

Sauran wadanda irin haka ta rutsa da su na da tasu damuwar.

Ishmael Daramy wani mai hako ma'adanin lu'ulu'u ne da aka datsewa hannayensa, ya ce: "Ina so ne a daure Charles Taylor a gidan yari, domin dai ba adalci ba ne Charles Taylor na ta more rayuwarsa ni kuma gani nan ina yawo tsirara a tituna.

"Ta yaya zan manta da wannan? Wata kila na iya yafewa, amma tabbas ba zan taba mantawa ba".

A gefen birnin Freetown, mazauna kauyukan ne dai ke ta faman neman nasu kason na wannan arzikin ma'adanan da Allah Ya yiwa Saliyo.

Wadansu mutanen na tsaye a ruwa, kusan iya kugunsu, suna wanke yashin da suka debo a ruwan, da zummar samun lu'ulu'u.

Tsintar ma'adanin dai ya kan kasance wani abin alfahari, sai dai kuma wannan kan tunasar da mutane tashin hankalin da duwatsun suka haddasawa kasar.

Aloysius Wai, wani dan kasuwa a kasar, ya ce, "Lu'ulu'u ya kasance annoba dari bisa dari. Idan har ana kashe mutane a saboda shi, ana sayen makamai da kuma lalata rayuwar yaran da ke tasowa, to tabbas kam ya kasance annoba".