Ana ci gaba da samun ambaliya a Pakistan

Wasu daga cikin mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Pakistan
Image caption A makon gudan da ya gabata, ambaliyar ruwa ta rutsa da mutane miliya hudu

Ambaliyar ruwa na kara kwarara a wasu yankunan kasar Pakistan yayin da ake ci gaba da sheka ruwan sama mai kama da bakin kwarya.

Kogunan da ke Lardin Sindh a tsakiya da kuma kudancin kasar ta Pakistan sun cika sun batse yayin da ruwan ke gangarawa zuwa teku.

Tuni dai aka umurci dubban mutane da al'ummun da ke yankin Kogin Indus a lardin na Sindh su bar gidajensu.

A duk shekara dai a kan samu ambaliyar ruwa a Sindh, amma ba a taba samun ruwa mai yawan da ake zaton za a samu a 'yan sa'o'i masu zuwa ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa a mako gudan da ya gabata mutane dubu da dari shida ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan.

Ta kuma ce ambaliyar ta rutsa da mutane miliyan hudu.

Ruwan dai ya wanke hanyoyi da gadoji, ya kuma rusa dubban daruruwan gidaje.