Bukin tunawa da harin nukiliya a Hiroshima

Jakadan Amurka a Japan, John Roos
Image caption A karo na farko, jakadan Amurka a Japan, John Roos, ya halarci bukukuwan

A kasar Japan, ana can ana bukukuwan tunawa da harin bom din da Amurka ta kai da makamin nukiliya a kan garin Hiroshima shekaru sittin da biyar da suka wuce.

Dubun dubatar mutane ne dai suka hallara a garin na Hiroshima don sauraron kararrawar zaman lafiya wadda aka kada a daidai lokacin da Amurkar ta saki bom din, wanda ya hallaka kusan mutane dubu dari da arba'in.

Daga cikin mutanen da suka hallara har da wadanda suka tsira da raukansu a ranar ta 6 ga watan Agustan shekarar 1945, wadanda kuma suka yi hadaya da ruwan sha ga wadanda kishi ya kashe a ranar.

Haka nan kuma a karo na farko, jakadan Amurka ya halarci wurin bukukuwan.

Sauran wadanda suka je wurin sun hada da wakilan Birtaniya, da Faransa, da kuma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, wanda ya shaidawa BBC cewa:

“Na zo ne da sakon kyakkyawan fatan samun zaman lafiya. A halin yanzu muna kan wata mahada inda wajibi ne mu tabbatar da an kawar da makaman nukiliya daga doron kasa”.