Hari aka kaiwa jirgin ruwan Japan a mashigin Hormuz-inji masu bincike

Masu bincike sunce jirgin ruwan daukan man nan na Japan da ya lalace a mashigin ruwa na Hormuz a cikin makon da ya wuce, 'yan ta'adda ne suka kai masa hari.

Jami'an tsaron gabar teku a Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce sun gano burbushin wani bam da aka hada a gida a bodin jirgin ruwan mai suna M Star.

Daya daga cikin ma'aikatan jirgin ya dan samu rauni.