Za a rubuta taken Kudancin Sudan

Taswirar Sudan mai nuna yankin Kudancin Sudan
Image caption Mahukuntan Kudancin Sudan sun bukaci mawaka su rera sabon taken yankin

An bukaci mawaka da kuma marubutan yankin Kudancin Sudan su rubuta, su kuma rera sabon taken kasa.

Kakakin tsohuwar kungiyar 'yan tawaye ta SPLA, Malaak Ayuen Ajok, ya ce za a shirya gasa don zabar wanda ya fi dacewa ya zama sabon taken kasa na yankin na Kudancin Sudan.

A watan Janairu mai zuwa ne dai yankin na Kudancin Sudan zai kada kuri'ar raba-gardama a kan ballewa, ko kuma ci gaba da kasancewa a cikin kasar ta Sudan.

Mista Ajok ya ce rubuta sabon taken ba ya nuni da sakamakon da hukumomin yankin Kudancin Sudan din ke so.