An harbe ma'aikatan lafiya goma a Afghanistan

Karen Woo, Likita a Afghanistan
Image caption Karen Woo, Likita a Afghanistan

An harbe wasu ma'aikatan lafiya su goma har lahira a lokacin da aka yi wa ayarin motocinsu kwanton bauna a arewa maso gabacin Afghanistan.

Sun hada da Amerikawa shida da wasu 'yan kasashen wajen guda biyu, da kuma 'yan Afghanistan guda biyu.

Kungiyoyin Taleban da Hezbi Islami sun ce sun kashe 'yan kasashen wajen ne saboda suna kokarin sanya Musulmi yin ridda da kuma yi wa Amurka leken asiri.

Babban Darektan kungiyar agaji ta Kirista da ta dauki mutanen aiki, Dirk Frans, ya ambaci yadda matsalar tsaro za ta iya shafar aikin nasu.

Ya ce, "Idan har batun tsaro ya zama babban abin damuwa gare mu, ina ganin ba za mu cigaba da aiki a Afghanistan ba."