An ranstar da sabon shugaban kasar Colombia

Image caption Shugaba Santos na kasar Colombia

An rantsar da Juan Manuel Carlos Santos a matsayin sabon shugaban kasar Colombia na arbain a bikin da aka girka tsaro sosai, kuma wanda ya samu halatar mafiyawa daga cikin shugabannin yankin Latin Amurka.

A jawabinsa yayin rantsar da shi, sabon shugaban kasar Colombia , ya bayyana cewa, inganta dangantaka tsakanin kasarsa da makwabtanta wato kasashen Ecuador da kuma Venezuela, shine zai kasance daya daga cikin manyan abubuwanda gwamnatinsa za ta sa gaba.

Dukkanin kasashen sun yanke huldar jakadanci ne da gwamnatin Colombia karkashin jagorancin Alvaro Uribe.

Amma kuma sabon shugaban kasar ya ce watakila, zai tattauna da dan 'yan kungiyar Marxist masu tada kayar baya a kasar akan yadda za'a cimma sulhu.