Motoci sun gamu da cikas a jihar Jigawa

Image caption Gwamnan Jihar Jigawa

A Najeriya zirga zirgar motoci tsakanin wasu jihohin Arewa maso gabashi zuwa Arewa maso yammacin kasar sun gamu da cikas sakamakon yankewar wani sashe na titin Kano zuwa Bauchi.

Lamarin ya auku ne a tsakar daren jiya ne sakamakon wani gagarumin ruwan sama da akayi ,wanda ya sa titin ya rufta a wani yanki na karamar hukumar Birnin kudu dake Jihar Jigawa.

A yanzu dai masu motoci suna kewayawane ta wani sashe na jihar jigawan sukai ga wuraren da zasu,yayinda gwamnatin jihar Jigawan ta dukufa daukar matakin wucin gadi na gyaran hanyar kafin gwamnatin tarayya ta gyara.