Hukumar ICPC ta fara bincikar gwamantin jihar Kebbi

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta a Najeriya, ta ce ta soma bincike kan wani koke da wasu 'yan siyasa daga kanana hukumomi shidda na jahar kebbi suka kai a gabanta.

Masu koken dai suna zargin gwamnan jahar Alhaji Saidu Usman Dakin Gari da wasu kwamishinoninsa biyu da kuma wani dan uwansa da yin almundahanar kudi Naira miliyan 470 daga asusu kananan hukumomi da sunan aiwatarda wasu aiyukkan da suka ce ba'ayi ba.

Sai dai jami'an gwamnatin jihar sun musanta zargin , sun kuma ce a shirye suke ,su kare kansu a gaban hukumar.