Madatsun ruwa na cikin hadarin fashewa a Pakistan

Jami'ai a Pakistan sun ce madatsun ruwa guda biyu suna cikin hadarin fashewa saboda karfin ruwan da ke ambaliya daga koramu da koguna a lardin Sindh da ke kudancin kasar.

Suka ce sa'o'i ashirin da hudu na tafe na da matukar tada hankali ga rayuwar mutane dubu dari hudu.

An soma aikin sake ginin wasu gadoji da hanyoyi.

Sai dai Muhammad Irfan, ya ce ambaliyar ruwan na kawo cikas ga wannan aiki.

Ya ce, "Gwamnati ta mayar da hankali cikin hanzari wajen gyara karyayyun gadoji.

Kamfanoni da dama suna aiki a kansu, sai dai ruwa ya yi yawa yadda aikin gyaran yake zama mai wuyar gaske."