Rasha ta zargi Amruka kan yarjejeniyar rage makamai

Shugaban Rasha Dmitriy Medvedev

Rasha ta zargi Amurka da karya alkawarin da ta yi a kan yawan makaman da suka yi yarjejeniyar za ta rage.

Ma'aikatar Harkokin waje a Moscow ta fitar da wani jawabi mai shafi bakwai, inda take zargin Amurka keta alkwarin da ta yi a yarjejeniyar rage makamai da kuma sinadarai masu guba, da ma sauran makamai masu illa ga lafiyar bil adama.

A halin yanzu dai babu tabbas a kan abin da ya sanya Rasha yin wannan jawabi.